Wasu mutane biyu sun bayyana gaban wata Kotu a birnin London yau Laraba bisa zargin ayyukan ta’addanci, ana zarginsu da kulla makarkashiyar kashe firayin ministar kasar Burtaniyya Therasa May, a cewar jami’an gwamnatin kasar.
Jami’ai sun ce mazajen biyu sun kulla makarkashiyar yadda zasu kai harin wuka a unguwar Downing, inda gidan Firayin ministar yake.
Rahoton kulla kai harin wanda aka dakile ya bayyana ne jim kadan bayan da shugaban hukumar binciken sirrin cikin gida ta Burtaniyya Andrew Parker, yayi ma ‘yan majalisar kasar bayani kan barazanar ‘ta’addanci da kasar ke fuskanta, ya kuma sanar da ministocin kasar cewa hukumarsa ta sami nasarar bankadowa da hana kai hare-haren ta’addanci guda 9 a cikin shekarar nan.
Ya bayyanawa ministocin kulla kai harin a lokacin wani zama, koda yake dai ba a ba ‘yan jarida labarin ba sai bayan sa’o’i.
Facebook Forum