Jumma’a majalisar dokokin Thailand ta zabi Yingluck Shinawatra, mace ta farko Frayin ministan kasar, wata daya bayan da jam’iyyar ta sami gagarumin nasara a zaben kasar da aka yi ranar uku ga watan jiya.
A majalisar wakilai ta kada kuri’a 296 na goyon bayan zabenta, wakilai uku suka ki amincewa, wasu 197 suka kauracewa jefa kuri’a.
‘Yar shekara 44 da haifuwa, Yingluck ta shiga siyasa ne cikin watan Yuni, kuma kanuwar tsohon PM Thaksin Shinawatra ne, mutumin da aka yi wa juyin muli cikin ruwan sanyi a 2006, kuma yanzo yake zaman gudun hijira ta kashin kansa.
Kamin ta kama aiki sai sarki Bhumibol Adulyadej ya amince da nadinta a wani biki na daban da ake sa ran gudanarwa cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.