Wannan kora da aka wa mayakan na Boko Haram a sansaninsu da ake kira Camp Zero na zuwa ne a daidai lokaicn da mayakan suka zafafa hare-harensu a arewa maso gabashin Najeria.
A baya-baya nan mayakan na Boko Haram, sun kai hari jihar Adamawa a Madagali inda aka yi asarar rayuka da dama, kana wasu suka jikkata.
Sambisa wani katafaren daji ne da ya ke da girman kilomita 1,300 a arewa maso gabashin jihar Borno.
Ya kuma dangana da wasu jihohi da suka hada da Yobe da Gombe da Jigawa da wani yankin Kano.
Dakarun Najeriya sun jima suna fafutukar neman kwace wannan daji, wanda ya zama tunga ga mayakan.
Yayin da wasu masana ke jinjina wannan namijin kokari da dakarun Najeriya suka yi, wasu kuwa na yin kiran a yi taka-tsantsan ne.
Fargabarsu ita ce kada a bari mayakan na Boko Haram su sake hadewa a wata tunga ko kuma su fantsama cikin al’uma.
Sai dai yayin da rahotanni ke ruwaito hukumomin Najeriya na nuna cewa dajin na Sambisa ne gaba daya ya kubuce a hanun Boko Haram, wasu na cewa babbar tungar mayakan ce aka karbe, wato Camp Zero.
Domin jin irin fashin bakin da masana ko kuma kwararru ke yi danagne da wannan lamari, saurari rahoton wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka, Hassan Maina Kaina daga Abuja.
Sannan bayan rahoton za ku ji tattaunawar wakilin Muryar Amurka a Kano Mahmud Ibrahim Kwari da Manjo Hassan Mai ritaya inda ya fara da tambayar shi yadda ya ke kallon daukacin lamarin na kwato dajin Sambisa.