A hirar da aka yi da Daya daga cikin na hanun damar sheik Ibrahim El-Zakzaky, jagoran mabiya mazhahabar ‘yan shi’a ta wayar tarho bayan salar Idi, Dr. Abdullahi Danladi yace, “an gama hidimar sallah lafiya kuma komai ya koma daida kamar da.
Akan wadanda suka rasa rayukansu kuma, Dr. Abdullahi yace, akallah akwai mutane talatin da uku wadanda suka rasa rayukansu banda wadanda suka samu raunika masu tsanani wanda a a halin yanzu ana kan yi masu magani.
An sami sabanin ruhotanni akan musabbabin wannan al’amari, amma wani ganau wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya agaya ma manema labarai cewa, “a lokacinda suke bada hanu akan hanya, sai sojojin suka tare hanya. Sukuma sai suka bukaci a barsu su gama aikin su amma sojojin suka bude masu wuta.
A tattaunawar da sheik Ibrahim EL-Zakzaky yayi jiya a zaria da manema labarai ya ce, “wannan abinda ya faru ya nuna cewa, an maida mu Gaza. Abinda Isra’ila ke ma falasdinawa, shi ake mana". Kamar yadda zaku ji, wakilin muryar Amurka a kaduna Nasiru Yakubu birnin Yero shine ya bada ruhoton.