Cutar na kama dan Adam ne ta hanyar ta'ammali ko ta farautar namomin daji.
Wanda ya kamu da cutar zai iya yadata zuwa sauran mutane da suke kusa dashi.
Alamun kamuwa da cutar sun hada da zazzabi mai zafi da kasala da amai da gudawa. Amma kafin ciwon yayi nisa alamunsa bashi da banbanci da cutar cizon sauro. Daga baya idan ciwon yayi nisa sai mutum ya fara amai jini kuma na fita ta hanci ko baki ko kuma a gudawa. Ciwo ne mai zafi kuma yawancin wadanda suka kamu dashi suna mutuwa.
Matakan kariya na farko su ne duk dabbar da bata da lafiya ko ta mutu mushe to a kaurace mata. A kona mushen ko a binne shi. Kada mutane su yi ta'ammali dashi. San nan kuma duk wani nama ma a tsaftaceshi, a wankeshi kuma a ingantashi. A kula cewa amayanka dabbobi masu lafiya za'a shigo dasu.
Dangane da masu cin namun daji da aka sani da suna "bush meat" bisa ga gaskiya abu mafi a'ala shi ne a kauracewa cin irin wannan naman har a shawo kan cutar domin a wadannan namomin ake samun cutar.
Masu kiwon dabbobi a gida irin su birai idan basu fita waje ba to a kira masu kulawa da lafiyar dabbobi su duba idan akwai alamar cutar garesu domin a yi maza a kare dabbar.
Masu kula da wadanda cutar ta kama to su dinga sa safar hannu da rigunan kariya. Ban da haka duk lokacin da mutum ya gama ya wanke hannunsa. Kada kuma abata lokaci kafin a kai ga asibiti.
Ga karin bayani.