Yakin neman tsayawa takarar shugabancin Amurka karkashin tutar jam’iyar Republican da na Democrat ya koma neman wakilai da zasu je babban taron jam’iyun na kasa, inda jam’iyun zasu tsayar da ‘yan takararsu a zaben shugaban kasar da za a gudanar a watan Nuwamba.
Hamshakin dan kasuwar nan Donald Trump shine ke kan gaba a jam’iyar Republican sai dai ya fada ranar Litinin cewa, shugabannin jam’iyar sun kirkiro wata hanyar coge domin hana shi nasara a babban taron jam’iyar da za a gudanar a Cleveland Ohio. Ko da yake Trump ne ya lashe zabe a galibin jihohi, bashi da isassun wakilai da yake bukata na zama dan takarar jam’iyar.
A bangaren democrat kuma, tsohuwar jami’ar diplomasiyar Amurka HIllary Clinton ta yiwa abokin hamayyarta dan majalisar dattijai mai wakiltar jihar Vermont Benie Sander fintinkau a yawan wakilai, sai dai ita ma har yanzu bata sami isassun wakilai da take bukata na zama ‘yar takarar jam’iyar ba.