Bisa la'akari da yadda jamhuriyar Nijar take kewaye da tashe tashen hankula yanzu haka shi yasa kungiyar Cocin Katolika ta jamhuriyar Nijar ta shirya wani zaman taro wanda ya hada manya limaman Islama dana Kirista domin fadakawa akan sha’anin zaman lafiya a cikin jamhuriyar ta Nijar.
Shugaban Cocin Katolikan Maradi, ya ce wannan taro ne na bada horo wanda ya shafi Malamai na addinin Kirista dana Musulunci domin su gane mahimmancin zaman lafiya a cikin kasa, kuma kar wani ya tashi gobe ya ce yana iya kawo illa gad an uwansa wai domin addinin sub a daya bane.
Shima Malam Muhammadu Dan Wazifa ya ce taro wani mataki ne na tattaunawa domin a gano shin dame dame ke kawo tashin hankali ko zaman lafiya.
Taron dai ya dauki kwanaki hudu a gudanar da shi a birini Kwanni kuma ya hada Malaman addinan biyu da suks fito da sassa daban daban na jihohi 8, na jamhuriyar ta Nijar.