Gwamnonin yakin kudu maso gabashin Najeriya sun kamala taronsu a birnin Enugun Najeriya,Gwamnonin dai sun bada tabbacin cewar zasu fuskanci batun shawo kan yunkurin kafa jamhuriyar Biafra, gadangadan.
Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, shugaban kungiyar Gwamnonin yanki, kuma ya karanta jawabin bayan taron.
Inda yake cewa lalle sun tattauna batun kungiyar MOSSOB, dake rajin ballewa daga Najeriya, kuma mun yake shawarar tuntubar kungiyoyi daban daban da Sarakunan gargajiya da shuwagabanin Addini da dai sauran masu ruwa da tsaki domin neman irin nasu shawarwari ta yarda za’a samu zaman lafiya mai dorewa yankin kudu maso gabashin Najeriya.
Gwamna Okorocha ya kara da cewa sun yake shawarar kiran wani babban taro na gaggawa na masu ruwa da tsaki a birnin Enugu ranar Lahadi mai zuwa.
Taron zai hada duk illahirin ‘yan majalisar dokoki na kasa da Ministoci na yakin, kuma suna shawartar masu fafutukar kafa kasar Biafra, da cewar su rungumi zaman lafiya.
Yayin da Gwamnonin ke kamala taron su, ita kuwa runduna ta 82, ta Sojan Najeriya dake birnmin Enugu, ta kira wani taron manema labarai inda kwamandan rundunar Birgediya janar Ibrahim Attahiru, a wata takarda da ya sanyawa hannu ya gargadi ‘yan kungiyar ta Biafra, da cewa su shiga taitayinsu domin tura ta kai bango.