Milliard kokuma biliyan 2050 da ‘yan ka na kudaden cfa ne gwamnatin ta Nger ke bukata domin tafiyar da aiyukanta a shekarar 2019 kamar yadda yake rubuce a tsarin kasafin da ministan kudin kasar HASSOUMI MASSAOUDOU ya fayyacewa ‘yan majalisa .
Dan Majalisa IRO SANI mataimaki na farko na shugaban majalisar dokokin kasa ya ce ayyukan da za’a fi ba karfi sun hada da ilimi wanda shi ne akan gaba, sai kuma gine-gine irin su hanyoyi da ba da wutar lantarki. Kacokan dai ayyukan gina kasa za su lakume wajen kashi 17 na kasafin kudin na shekarar 2019. Baya ga haka akwai kiwon lafiya da zai ci kashi 9. Yace kusan kashi 53 na kasafin kudin zai fito ne daga kasar ta hanyar haraji da sauransu.
Sai dai kakakin marassa rinjaye a majalisar.ISSAKA ISSOUHOU yace ba zasu yi kasa a gwuiwa ba wajen binciken kasafin na badi domin tabbatarwa kansu ba a mayarda bukatun talakkawa share ba.
Ya ce harajin da aka sa bisa abinci da sufuri har yanzu ba’a dakatar ba. Kudin lantarki ba’a rageshi ba. Haka ma na ruwa.
Masu wakiltar ‘yan Niger mazauna ketare a majalisar dokokin kasa sun bayyana anniyar bayarda gudunmawa wajen ganin gwamnatin ta hada kan kudaden da ta kudurta kashewa kasa a shekarar mai kamawa kamar yadda Dan Majalisar HARUNA DAI DUKA ya shaida.
Biliyan 78 da ‘yan kai na kudaden sefa ne gwamnatin ta kara akan kasafin shekarar 2018 domin kasafin na 2019 saboda ta hango wasu sabbin hanyoyin samarda kudaden shiga daga hannun wadanda biyan haraji ya rataya a wuyansu.
To amma masu rajin kare hakkin jama’a na ci gaba da tur da dokar harajin shekarar da muke ciki saboda suna ganin ta kutuntawa jama’ar kasar.
A sarari rahoton Souley Barma
Facebook Forum