Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kakakin Hukumar Kwastan Ya Ce Suna Kama Haramtattun Kaya Ne


John Attah kakakin hukumar kwastan
John Attah kakakin hukumar kwastan

Biyo bayan korafe korafen da jama'a su keyi akan yadda hukumar kwastan ke kama kaya ta ajiyesu a rumbunanta idan kuma ta tashi sayar dasu sai a samu wasu sun baci ko kuma sun wuce lokacin da yakamata a yi anfani dasu dalili ke nan da Muryar Amurka ta zanta da kakakin hukumar

A firarta da kakakin hukumar kwastan John Attah, Muryar Amurka ta ce akwai korafe korafe da yawa akan yadda hukumar take kwace kaya da motoci daga mutane.

John Attah dake magana da yawun hukumar kwastan ya ce ba kwace suke yi ba kamawa su keyi. Yace doka ta basu izinin kama duk kayan da aka shigo dasu ba kan ka'ida ba. Da zara sun sabawa dokar kasa za'a kamasu. Misali doka ta hana shigo da shinkafa ta kan iyakoki amma ta yadda a shigo da ita ta jiragen ruwa. Ma'ana, shinkafar da aka shigo da ita ta kan iyaka idan an kama ta zama kayan gwamnati kuma wanda ya shigo da ita zai fuskanci hukumci.

Idan mutum ya shigo da kaya kan ka'aida amma kuma ya ki biyan haraji dole ne su kama kayan har a biya ko kuma ya zama na gwamnati. Haka ma duk motar da aka shigo da ita ta kan iyaka idan an kama ta zama ta gwamnati. Amma idan ya shigo da ita ta tashar jirgin ruwa haraji kawai zai biya.

Akan motocin da hukumar ta tara a wasu garuruwan kasar, John ya ce sun fara yin gwanjo motocin ta yanar gizo kamar yadda doka ta basu izinin yi. Kawo yanzu mutane fiye da 7000 sun saye motocin dake Ibadan, Sokoto, Katsina da Lagos. Akan yin anfani da yanar gizo John Attah ya ce domin gujewa yin cuwa-cuwa ya sa suke anfani da yanar gizo.

Ga cikakken firar da Medina Dauda ta yi da John Attah na Hukumar Kwastan

please wait

No media source currently available

0:00 0:11:41 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG