Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Hada Kan ‘Yan Asalin Ghana Da Na Mazauna Kasar

Taron Hada Kan ‘Yan Asalin Ghana Da Na Mazauna Kasar
Taron Hada Kan ‘Yan Asalin Ghana Da Na Mazauna Kasar

Tsohon shugaban kasar Ghana, kuma ‘dan takaran shugaban kasa na babbar jam’iyar adawa ta NDC a zaben 2024, John Dramani Mahama, ya yi kira ga ‘yan kasa mazauna Zango da suka kai shekarun kada kuri’a da su je su yi rijistar katin zabe da ake gudanarwa.

ACCRA, GHANA - Tsohon sbugaban ya kuma gargadi jami’an zabe da su daina nuna wariya ga mazauna Zango, musamman domin sunayensu.

Taron Hada Kan ‘Yan Asalin Ghana Da Na Mazauna Kasar
Taron Hada Kan ‘Yan Asalin Ghana Da Na Mazauna Kasar

Zango wani mazauni ne ko matattara na al'ummomi masu matsakaicin karfin arziki daga Arewaci da kudancin Ghana, da kuma mafi yawanci, baki da suka yi gudun hijira daga kasashen Afirka ta Yamma shekaru da dama da suka gabata.

Tsohon shugaban kasa John Mahama, a wajen taron masu ruwa da tsaki da jam’iyar NDC reshen Zango ta shirya domin jin kukan mazauna Zangunan Accra, don a kara cikin manufofin jam’iyar kafin zaben 2024, ya ce matsalar da ‘yan Zango ke fuskanta na banbanci da wariya da ake nuna musu a wajen yin katin zabe da ake gudanarwa yanzu bai dace ba, domin tarihi na nuni da cewa, ‘yan Zango suna cikin Ghana shekaru da dama kafin Ghana ta samu ‘yancin kanta.

Taron Hada Kan ‘Yan Asalin Ghana Da Na Mazauna Kasar
Taron Hada Kan ‘Yan Asalin Ghana Da Na Mazauna Kasar

Domin haka idan aka kira sunan mutum,an gane kamar Fulani ne, ko Zabarma ne ko Bahaushe ne sai a ce ba ‘yan Ghana bane. Amma idan aka dubi tarihin kasar, ya ce kakanninmu sun zo nan tun karni na goma sha hudu, don haka kada a nuna babanci domin sunan mutum ya kasance haka, ace ba za a iya yi musu rijista ba.

Wasu masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun bayyana bukatunsu da suke da burin a cika musu. Kamar daya daga cikin wakilin sarakunan Zango, Sarkin Zabarmawan nima, Sai’du Luis ya ce, Majalisar Sarakuna na da fili da suka ajiye domin gina makaranta, suna bukatar jam’iyar ta gina musu makarantar idan ta hau mulki.

Taron Hada Kan ‘Yan Asalin Ghana Da Na Mazauna Kasar
Taron Hada Kan ‘Yan Asalin Ghana Da Na Mazauna Kasar

Jakadiyar Sarkin Hausawan Accra a nata bangaren ta ce a kula da matasa sannan kuma a magancewa Musulmai matsalar wajen ajiye gawa; ta kuma ce a yi shi yadda ya dace da Musulunci.

Taron Hada Kan ‘Yan Asalin Ghana Da Na Mazauna Kasar
Taron Hada Kan ‘Yan Asalin Ghana Da Na Mazauna Kasar

Taron ya samu halartar limamin limamai na Ghana, Dr. Usman Nuhu Sharubutu, da limamin Ahlul Sunna wal Jama’a, Shaikh Umar Ibrahim, da wakilcin Majalisar Sarakunan Zango da Kungiyoyin fararen hula daban-daban na Zongo.

Saurari cikakken rahoto daga Idris Abdullah:

 An Gudanar Da Wani Taron Hada Kan 'Yan Asalin Ghana Da Na Mazauna Kasar.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG