‘Yan takara guda hudu ne suka rage, wadanda ke neman tsayawa dan takarar shugaba na jam’iyar Republican. Yau talata cikin ikkon Allah, kusan za’a yi ta, a gama domin kuwa ranar ce da ake gasa sosai tsakanin tsohon gwanan jihar Massachusetts Mitt Romney da baban abokin hamaiyarsa Rick Santorum tsohon Senata.
Mitt Romney yana sa ran yin nasarar a jihohin Massachusetts da Vermont da kuma Virginia, yayinda shi kuma Santorum yake fatar samun nasara a jihohin Oklahoma da Tennessee.
Dukkan yan takara guda biyu sun yi yakin neman zaben ba kama hannu yaro, domin samun nasara a jihar Ohio inda kiddigar ta nuna cewa ana keke da keke wajen farin jinni, tsakanin yan takarar guda biyu.
Romney ya ci gaba da samu goyon baya daga shugabanin jam’iyar Republican, a saboda haka yake fatar samun galaba a zaben na yau.
Yace, yawancin yan Republican suna fadin cewa, suna son su fitar da jam’iyar Democrat daga fadar white House. A saboda haka suna son mutumin daya fahimci tsarin tattalin arziki a zaman wanda zai iya karawa da shugaba Barack Obama.
hi kuma Senata Santorum yayi aikin neman zaben data auna kuri’ar masu ra’ayin rikau wadanda har yanzu suke tababan aniyar Romney akan ra’ayin rikau. Ga abinda Santorum yace.
Yace suna bukatar sanin inda suka dosa a wannan zabe. Yace suna son mutumin da zai iya zuwa ya nuna makomar Amirka inda kowa zai ci moriyar tattalin arzikin kasa.
Shi kuma tsohon kakakin Majalisar wakilai, Newt Gingrich yana fatar cewa idan yayi nasara a jiharsa ta Georgia hakan zata karfafa masa gwiwa da kara masa karsashi. A Wannan makon Newt Gingrich ya fadawa gidan talibijin na ABC cewa idan ya samu nasarar a jihohin kudancin Amirka, hakan zata sa a yi tababar iyawar Romney na samun jam’iyar Republican ta tsayar dashi.