Masana ilimi da iyaye na ci gaba da tsokaci tun bayan da hukumomin Najeriya suka bayyana ka'idojin sake bude makarantun kasar wadanda aka rufe su sanadiyyar cutar COVID-19.
Tsokacin masu ruwan da tsaki kan harkar ilimin na zuwa ne yayin da hukumomin Najeriyar ba su bayyana takamaiman ranar da za a bude makarantun ba duk da cewa sun fitar da ka'idojin.
"Mutane da yada sun nuna damuwa da fushinsu kan cewa ba za a yi jarabawar WAEC kuma ba za a bude makarantu ba." In ji wani mahaifi Sanata Mas'ud El Jibril Doguwa.
Masu bincike akan harkokin ilimi a kasar sun bukaci hukumomin harkokin ilimin na Najeriya da su guji kwaikwayon kasashen ketare a yayin tsare -tsaren bude makarantun.
"Tun da gwamnati tana da hakki na kare lafiyar jama'a ya kamata ta yi duk abin da za ta yi ta kare lafiyar al'uma." In ji Malam Ado Ibrahim Kurawa, wani mai bincike a fannin ilimi.
Wata sanarwa da ministan ilimin Najeriya Malam Adamu Adamu ya fitar a ranar Litinin din nan, ta ayyana samar da tazara tsakanin dalibai da rage cunkoson dalibai a aji da kuma tabbatar da tsaftar makaranta da ta dalibai a matsayin wasu daga cikin ka’idodjin da ke kunshe a cikin daftarin matakan kare lafiyar dalibai da malamai da sauran ma’aikatan makarantu.
Ma'aikatar ilimin kasar ce ta samar da Wannan tsari bisa hadin gwiwa da ma’aikatun lafiya da na muhalli da kuma kwarrraru a tannin kiwon lafiyar al’umma.
Hakan dai na zuwa ne kasa da mako guda, bayan da kafofin labaru suka ruwaito ministan ilimin na najeriya na cewa, makarantun kasar zasu ci gaba da kasancewa a rufe har baba ta gani, la’akari da yadda cutar corona ke ci gaba da yaduwa a wasu sassan kasar.
Tuni dai wasu ke bayyana ra’ayin cewa, akwai alamun hukumomin ilimi a Najeriya sun shiga yanayi na kwam gaba kwam baya game da makomar ilimin kasar bayan corona.
Yanzu dai ‘yan Najeriya na ci gaba da dakon sanarwa ta gaba game da kokarin bude makaratun kasar.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Facebook Forum