Hukumar yaki da cin hanci da rasahwa a Najeriya EFCC ta damke wani Maxim Lobaty dan asalin kasar Rasha tare da wadansu ‘yan Najeriya biyu Austin Emenike da Nonso Onuchukwu a jihar Legas, akan laifin yi wa jama’ar Najeriya kusan dubu bakwai zamba har su ka karbi zunzurutun kudi Naira biliyan uku da sunan yin wata sana’a.
A cewar jaridar Daily Post, Wannan kamen ya biyo bayan karar da mutanen da suka narka dukiyoyin su a ciki ke ta kaiwa .
Hukumar ta bayyana cewa ta samu nasarar kwato Naira miliyan 216 da dubu 402 daga kamfanin na Swiss Golden.
“Daga bisani kuma an garzaya da mutanen uku zuwa jihar kano inda za a ci gaba da bincikar su.” Wani bincike ne dai ya bankado asirin wannan badakalar kudin da kamfanin Swiss Golden ke yi na yi wa jama’a wayo da karbe musu kudadensu”
Bayan kace-nacen da akayi a ofishin kamfanin da ke kano, Maxim da sauran wadanda ake zargi sun amince da su maida wa jama,a kudaden su amman a halin da ake ciki an samu Naira miliyan 216,402,565.05 a hanun su.
Ana ci gaba da binciken lamarin tare da kokarin hukunta duk wanda aka samu da laifin aikata hakan.
‘yan Najeriya da dama sun narka kudunsu a cikin wannan kamfani wanda yake da hawa hwa mai kama da wanda aka taba yi a baya mai suna bMMM.
Bayani a shafin kamfanin na yanar gizo ya nuna cewa wadanda suka shiga zasu sayi gwal ne su kuma ci gaba da tallata kamfanin tare da janyo wadansu mutanen su shiga.
Facebook Forum