Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sviatlana Ta Gudu Zuwa Kasar Lithuania


Sviatlana Tsikhanouskaya
Sviatlana Tsikhanouskaya

'Yar takara a jam’iyar adawa a kasar Belarus, Sviatlana Tsikhanouskaya ta ketara zuwa makwabciyar kasa ta Lithuania.

Hakan na faruwa ne bayan da aka kwashe kwana biyu ana fada tsakanin masu zanga zanga da ‘yan sanda biyo bayan zaben Shugaban Kasa.

Tsikhanouskaya, wadda ta ki amincewa da sakamakon zaben da aka bayana Shugaba Alexander Lukashenko, wanda ya dade yana mulkin kasa, ta ce barin kasar abu ne mawuyaci, amma tayi hakan ne saboda ‘ya’yanta.

“Na san da yawa zasu fahimce ni, wasu zasu kushe ni, wasu kuma zasu fara tsanata”, cewar Tsikhanouskaya.

"Kada Allah ya jarabce wani da abunda nake fuskanta, jama’a ku kula da kanku, abunda ke faruwa bai cancanci daukar rai ba."

Tun da farko a yau, Firai Ministan Luthuainia ya fadi cewa Tsikhanouskaya tana kasar kuma cikin koshin lafiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG