Kakakin shugaba Salvar Kiir na Sudan ta Kudu, ya yi ALLAH waddarai da rahoton hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD, wanda ya zargimanyan jami'an sojojin kasar ta Sudan ta Kudu masu yawa da aikata laifuffukan yaki.
A wata hira ta musamman a cikin shirin Muryar Amurka da ake kira South Sudan In Focus da aka yi jiya Alhamis, Ateny Wek Ateny yace rahoton na hukumar na cike da rudu, na bayanan da suka saba ma juna, abinda ka iya sake haifar da sabuwar koma baya ga kasar.
Rahoton hukumar Kare hakkin bil Adama ta MDD da aka fitar ranar 23 ga watan jiya, ya bayyana manyan jami'an soja su fiye da 40 wadanda majalisar ta ce kowannensu yana dauke da alhakin laifuffukan yaki da laifuffuka na cin zarafin bil Adama a Sudan ta Kudu.
Masu binciken ayyukan cin zarafin mutane sun tattara bayanai daga wurin shedun da suka ga wannan tuhumar da ake cewa an aikata ga fararen hula, wanda kuma mutanen dake sanye da kayan sarki ne suka aikata wannan aika-aikan, wadanda galibin su sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu ne.
Rahoton ya bada musalin wasu kwamandoji wadanda sune ke da alhakin kai munanan hare-hare a kan fararen hula a sassa daban-daban.
Sai dai Ateny ya ce idan wannan batu gaskiya ne to hukumar ta MDD ta mikawa gwamnatin Sudan ta Kudu sunayen wadannan jami'an sojan da ake zargi da kuma irin shaidar da ake da ita cewa sun aikata abubuwan da ake zarginsu.
Akan haka yayi fatali da wannan rahoton ya ce wanna na iya kawo wa kasar koma baya a yunkurin da take yi na shawo kan rikicin da ya addabeta.
Facebook Forum