Ma’aikatar kiwon lafiyar Sudan ta Kudu ta ayyana karshen annobar kwalara a cikin kasar bayan da ba’a samu labarin wani ya kamu da cutar ba, har tsawon makoni bakwai. Kungiyoyin bada taimako sun ce matakai da dama ne suka kawo karshen yaduwar wannan muguwar cuta a kasar da yaki ya daidaita.
Sun ce matakan sa ido mai inganci ne wuraren da da aka samu bular anobar cutar, yayin aka tura rukunin ma’aikatan jinya na sha yanzu domin gudanar da bincike a wuraren su kuma duba wadanda suka harbu. Sun ce kokarin samar da ruwamai kyau, da wayarwa jama’a kai akan muhimmancin tsafta da kuma jinyar wadanda suka kamu da kwalara, sune matakan da suka taka rawar gani wurin kawo karshen cutar.
Jerin gudanar da ayyukan bada alluran rigakafi a bara ya bada gudunmuwa ga kawo karshen cutar. Hukumar bada allurer rigakafi ta kasa ta kasa ta GAVI, ta digawa mutane sama da miliyon biyu da dubu dari biyu maganin rigakafin cutar.
Mai Magana da yawun hukumar GAVI, James Fulker, ya fadawa Muryar Amurka cewa, rigakafin da ke bada kariyar sheakru biyar, an baiwa mutane sama da miliyon daya, amma kuma yace shirin allurar rigakafin ya huskanci matsalar kayan aiki.
Sai dai Fulker yayi kashedi a kan kada jin dadi ya sa mu manta da kanmu. Yace bular anobar kwalara a Sudan ta Kudu kuma tana kara yawa ko yaduwa a sakamakon rashin tsafta, da rashi ruwa mai kyau da rashin makewayi.
Kungiyoyin bada taiamko sun ce akwai yiwuwar sake bullar anobar kwalara a farkon wata Afrilu idan damina ta fara. Sun gargadi mutane da su kula da alamomin sake bullar anobar cutar.
Facebook Forum