Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Spain ta Bude Iyakokinta Ga Masu Yawon Bude Ido


Kasar Spain ta bude iyakokinta ga masu yawon bude ido da ke fitowa daga Turai, yayin da nahiyar ke ci gaba da sassauta matakan kulle da aka saka don yaki da cutar ta COVID-19.

A jiya Lahadi kasar ta Andalus ta fara daukan wannan mataki a wani yunkuri na maido da harkokinta yau dan kullum.

A da, Spain ce kasa ta uku da ta fi yawan masu dauke da cutar a duniya, amma yanzu ta koma matsayi na bakwai inda take da mutum dubu 246, 000 da aka tabbatar suna dauke da ita, kamar yadda Cibiyar binciken a jami’ar Jami’ar Johns Hopkins ta sanar.

Sai dai yayin da nahiyar ta turai ke farfadowa sannun a hankali, kasashe irinsu Brazil, Afirka ta Kudu, India, da kuma nan Amurka na ci gaba da ba da rahotannin samun karin masu harbuwa da cutar.

Baya ga Amurkan, Brazil ce kasa ta biyu a duniya da ta fi yawan masu cutar ta COVID-19 inda take da mutum sama da miliyan daya, yayin da Rasha ke matsayi na uku da mutum sama da dubu 576.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG