Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da a jihar Sakkwato kadai ma ‘yan bindiga suka hallaka mutane fiye goma sha daya; suka kuma yi garkuwa da wasu fiye da dari daya cikin kwana uku kacal.
Tabbacin kare rayuka da mahukunta ke bai wa ‘yan Najeriya ya kasa fitar fargaba daga zukatansu, saboda yanayin da suka tsinci kansu ciki a wasu wurare.
‘Yan bindiga sun kai hari da a wani kauye da ake kira Dan Gari dake kusa da garin Gatawa a karamar hukumar Sabon Birni dake jihar Sakkwato a arewa maso yammacin Najeriya, ranar Litinin ta wannan mako da rana tsaka.
Dan Majalisar Dokoki na jiha mai wakiltar yankin, Aminu Almustapha Boza, yace a lokacin maharan sun hallaka mutane 11 a garuruwa 3 kuma kullum sai sun kai hari sun kashe mutane ko sun yi garkuwa da su.
A karamar hukumar Gotonyo mai makwabtaka da Sabon Birni bayanai sun nuna cewa a cikin dare daya na ranar Litinin ‘yan bindiga sun sace mutane kimanin 60 a garuruwa daban daban na karamar hukumar.
Shugaban karamar hukumar Abdulwahab Yahaya Goronyo ya bayyana cewa yana wuya a iya tantance adadin mutanen da ake garkuwa da su a yankin domin kullum sai an kai hari a garuruwa daban daban, ya bukaci jama'a da su dage da addu'o'in samun daukin Ubangiji.
A karamar hukumar Gada mai makwabtaka da Goronyo dan majalisar yankin Kabiru Dauda ya ce jama'ar yankin na cikin mummunan hali, domin a cikin kwana 3 barayi sun yi garkuwa da mutane 5o daga mazaba daya kacal.
A lokacin baya da matsalar ta yi kamari a Sakkwato an gudanar da wani taro wanda ya hada muhimman mutanen jihar don tattauna matsalar.
Dan majalisar Sabon Birni Aminu Boza wanda yana cikin wadanda suka yi ruwa suka yi tsaki aka shirya taron, yace sun yi zaman tattaunawa akan matsalar amma daga karshe abin bai yi tasiri ba.
Kokarin ji daga jami'an tsaro ya ci tura, duk da yake karshen makon daga gabata ne kwamishinan ‘yan sanda a jihar ya kira taron manyan jami'ai na rundunar don tattauna sha'anin tsaro a lokutan bukukuwan kirsimati da sabuwar shekara hadi yekuwar neman zabe, kuma ya baiwa jama'a tabbacin kara jajircewar jami'ansa ga aikin samar da tsaro.
Yanzu dukanin kananan hukumomi dake gabashin Sakkwato na fuskantar mawuyacin hali da rashin tabbas ga rayukan jama'ar da ke zaune wuraren.
Saurari rahoton: