Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sokoto: Gobara Ta Lakume Daruruwan Shaguna A Kasuwar ‘Yan Katako

Wata gobara da ta tashi (Wannan hoton misali ne)
Wata gobara da ta tashi (Wannan hoton misali ne)

Gwamnan jihar Ahmadu Aliyu Sokoto ya kwatanta gobarar a matsayin “abu mara dadi da ya yi sanadiyyar haddasa asarar dukiya mai yawan gaske ga ‘yan kasuwar, wadanda suka dogara da wannan masana'anta.”

Wata gobara da ta tashi a ‘Yan Katako da ke Sokoto ta lakume shaguna sama da 500 a kasuwar .

Wutar ta fara ne cikin daren Talata wayewar garin safiyar Laraba inda ta yadu zuwa sashen ‘yan katako ta yi barna mai yawa.

Gwamnan jihar Ahmadu Aliyu Sokoto ya kwatanta gobarar a matsayin “abu mara dadi da ya yi sanadiyyar haddasa asarar dukiya mai yawan gaske ga ‘yan kasuwar, wadanda suka dogara da wannan masana'anta.”

Ya kara da cewa, “a madadin gwamnati da al'umar jihar Sokoto, ina mika sakon jaje ga wadanda wannan gobara ta shafa. Ku sani cewa muna tare da ku a wannan lokaci da wannan ibtila'i ya afka muku kuma za mu tallafa muku ta hanyoyin da suka dace.”

Wannan ibtila'in gobarar ya faru ne kasa da wata guda bayan wata wuta da ta lakume shaguna sama da 50a kasuwar ‘yan hatsi a Sokoto.

“Kari akan wannan, mun kafa wani kwamiti mai karfin gaske domin gudanar da bincike akan musabbabin tashin gobarar da kuma hanyoyin kare faruwar hakan a nan gaba. “ Gwamna Aliyu ya kara da cewa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG