Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SOKOTO: An Haifi Yara 'Yan Biyu Maza A Hade


'Yan Biyu Maza Da Aka Haifa A Hade, Sokoto
'Yan Biyu Maza Da Aka Haifa A Hade, Sokoto

An haifi yaro namiji, a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, wanda ya zo da gangar jiki daya, da kai biyu, idanu hudu, baki biyu da kuma hanci biyu.

Duk da yake abu ne wanda ba saban ba, amma wasu lokuta ana samun labarin haihuwar yara 'yan biyu ko 'yan uku wadanda ake haihuwa a hade, ko kuma wani sashe na jikin su hade, kamar yadda aka yi ta samu a kasashen duniya.

Wannan karon ma an haifi yaro namiji, a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, wanda ya zo da gangar jiki daya, da kai biyu, idanu hudu, baki biyu da hanci biyu.

A ranar Talata, 30 ga watan Janairun wannan shekara ne aka kai mahaifiyar yaron a asibitin mata da kananan yara da ke tsakiyar garin Sokoto da matsalar juna biyu, kuma ya kai lokacin haihuwa, sai bincike ya nuna da wuya ta iya haihuwar abin da ke cikinta.

Daya daga cikin ma'aikatan asibitin da suka yi fama da matar, Hafsat Muhammad Bazza, ta ce hoton cikin da aka yi ya nuna cewa jaririn da ke cikin mahaifar matar yana da babban kai saboda haka bazata iya haihuwar sa da kanta ba, dole sai an yi aiki an fitar da shi, sai aka shiga da ita dakin tiyata.

A lokacin da aka yi mata aikin tiyata sai aka fitar da yaro wanda ba'a saba ganin kalar saba.

Maryam Yusuf Muhammad daya daga cikin dangin mahaifan yaron kuma daya daga cikin wadanda ke hidima a asibiti lokacin haihuwar ta ce da aka fitar da yaron an tarar da yana da idanu hudu, baki biyu da hanci biyu, kuma bayan sa bude yake har ana ganin lakkar sa.

Mahaifin yaron Yusuf Abdullahi yana cike da al'ajabi ganin irin abubuwan da ake gani a wasu kasashe na duniya yau ga shi a gidan sa cikin iyalan sa, sai dai ya yi godiya ga Allah kuma ya nemi taimakon yadda zai iya kulawa da yaron.

Masana kiwon lafiya Dokta Umar Idris, likita ne a Sokoto, ya ce ana samun irin wannan lamarin kaloli mabambanta kuma yana faruwa ne a lokacin da ake halittar 'yan biyu, idan aka samu tsaiko wajen rabuwar su tun a cikin mahaifa.

A cewar masanin kiwon lafiyar babu abu daya da za'a ce shi ke haifar da hakan amma dai akwai wasu abubuwa da za'a ce su ne silar samar da hakan, wadanda suka hada da yanayin halitta na zuri'a, ko yanayin muhallin da suke ciki ko kuma shaye-shayen magunguna barkatai irin na gargajiya, ga masu juna biyu.

Wasu lokuta idan aka samu hakan bincike kan iya nuna ko za'a iya raba yaran da aka haifa hade, ko akasin haka.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG