Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

LAFIYA UWAR JIKI: Batun Mata Masu Karbar Haihuwa Da Kuma Irin Kalubalen Da Suke Fuskanta - Mayu 11, 2023


Hauwa Umar
Hauwa Umar

Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 5 ga watan Mayu na kowace shekara a matsayin ranar mata masu karbar haihuwa wato ungozoma ta duniya domin jinjina musu da kuma samar da sabbin hanyoyi da kuma dabarun kula da mata masu juna biyu da kuma jarirai tun kafin haihuwa har zuwa bayan haihuwa.

Hakan yasa shirin lafiya uwar jiki na wannan mako ya ji matsayin wannan rana ga mata masu karbar haihuwa da kuma irin kalubalen da suke fuskanta wajen gudanar da aikin nasu daga bakin Fatima Bako, ungozama dake aiki a asibitin mata da yara na Jihar Maradi a Jamhuriyar Niger.

Saurari shirin a sauti:

LAFIYA UWAR JIKI: Batun Mata Masu Karbar Haihuwa Da Kuma Irin Kalubalen Da Suke Fuskanta - Mayu 11, 2023
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:46 0:00

XS
SM
MD
LG