Wata cibiyar dake sanya ido a kan rikicin da ake yi a kasar Syria ta ce farmaki da sojojin gwamnati suka kai a jiya Talata a wata gunduma mai suna Ghouta dake hannun 'yan tawayen a bangaren gabashin Damascus, ya kashe sama da mutane dari.
Wata kungiyar rajin kare hakkin dan adama ta kasar Syria dake Birtaniya, tace akalla mutane 250 ne aka kashe tun daga yammacin ranar Lahadi, hari mafi muni tsakain sa’o’I 48 da aka kai a cikin yakin Syria, tun bayan harin guba da aka kaiwa gundumar a shekarar 2013
A jiya Talata, sojojin Turkiya sun tilastawa sojojin gwamnatin Syria suka koma baya, a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa yankin Afrin na kasar Syria, yankin da sojojin kasar ta Turkiyya take gwabza fada da dakarun Kurdawa har na tsawon wata guda.
Gidan talbijin na Syria ya nuno ayarin rokoki kimanin ashirin suna shiga yankin Afrin daga kauyen Nubul.
Aikewa da sojoji na zuwa ne wuni guda bayan da Turkiya ta yiwa gwamnatin Syria kashedi, kada ta shiga yankin, cewa zata mai da martani idan sojojin Syria suka yi kokarin kare mayakan Kurdawa.
Facebook Forum