Rundunar sojan Sudan tace ta fafata da yan tawayen da suke da alaka da sabuwar kasar kudancin Sudan a wata jiha mai muhimmanci wadda take kan iyaka.
A jiya juma’a kamfanin dilancin labarun kasar ya bada labarin cewa, gwamnati ta ayyana dokar ta baci a jihar Blue Nile kuma ta nada soja ya jagorancoi yankin, bayan da fada ya barke a yankin a ranar alhamis da dare.
Dukkan bangarorin suna zargin juna da laifin tsokanar tarzomar data auku a garin Al Damazine. Jiya juma’a gwamnatin Sudan tace ta fatattaki sojoji wadanda bisa al’ada suke biyaya ga kungiyar Sudan Peoples Liberation Army ko kuma SPLM a takaice.
Shedun gani da ido sunce a jiya juma’a mutane da dama suka arce daga garin Al Damazine. Hargitsin baya bayan tasa ana nuna damuwar cewa fafatawa tsakanin bangarorin biyu tana bazuwa daga jihar Kordofan wadda itama take kan iyaka.
Tun dai lokacin da yankin kudancin Sudan ya ayyana samun yanci daga kasar Sudan, arangamomi suka yi kamari a akan iyakokin yakunan. Jihohin Blue Nile da Kordofan suna cikin kasar Sudan, to amma yawancin mutane da suka goyi bayan yankin kudancin kasar a fafatwar shekaru ashirin da daya har yanzu suna zaune a wadannan jihohin.