Rundunar sojan Sudan tace ta gwabza da mayakan ‘yantawayen sabuwar kasar nan ta Sudan ta Kudu a wata jihar dake kan iyakokinsu. A ran Jumu’ar nan ne, gwamnatin Sudan ta bada sanarwar cewa ta kaddamarda zaman halin gaggawa a jihar ta Blue Nilu, har ma ta nada kantoman sojan da zai ja ragamar harakoki a yankin. Kowanne daga cikin sassan biyu yana dora laifin barkewar yakin a kan dayan sashen. Yanzu haka rahottani na nuna cewa mutanrn garin al-Damazine sun wuni suna arcewa don tsira da kansu daga wannan tashin hankalin.
Sabon tashin hankali a tsakanin kasashen Sudan biyu
- Aliyu Mustapha
![Sudanese army spokesman Sawarmi Khaled Saad speaks to reporters about the clashes between the Sudanese army and the Sudan People's Liberation Army (SPLA) in Blue Nile.](https://gdb.voanews.com/8ecc85ee-1181-4e46-80ea-e6457095e4f1_w250_r1_s.jpg)
An gwabza yaki tsakanin sojojin kasar Sudan da na sabuwar kasar Sudan ta jihar Kogin Nilu.