Kasar Rasha ta tabbatar da cewa wasu daga cikin sojojinta suna kasar Syria, a daidai lokacin da yammacin duniya ke fargabar cewa sojojin kasar Rashan na dada sa kan su wajen marawa gwamnatin Bashar Al’assad da ke fama da rikicin baya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ce ta fadi haka a wata sanarwa jiya Laraba. Ta fadi cewa sojojin nasu na Syria ne da nufn koyar da sojojin kasar lakantar amfani da makaman yakin Rasha da makamantansu.
Tace Rasha bata taba sirranta maganar fasahar hadin kan kerekeren sojojinta dana Syria ba, kuma tun tuni take samar mata makamai da na’urorin soji bisa yarjejeniyar fahimtar da ke tsakaninsu. Ta kara da cewa makaman da aka kai Syria din na nufin yakar ta’addanci ne.
Barazanar ta’addancin da ta kai kololuwar yadda ba a yi tsammani ba a kasar da kuma makwabciyarta ta Iraki.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka John Kirby yace, Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yayi Magana da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov game da damuwar Amurka akan lamarin.