Hukumomin tsaron Jamhuriyar Nijer da na Burkina Faso sun bada sanarwar hallaka ‘yan ta’adda sama da 100; sun kuma cafke wasu gommai tare da lalata kayaki da dama a yayin wani aikin kakkabar da dakarun kasashen 2 suka gudanar a yankunan da ke iyaka a cikin watan nan na Afrilu.
A yayin rawar daji ta hadin gwiwa da aka yi wa lakabi da operation Taanli 3 da ke nufin kawance a harshen gurmawa, wanda suka gudanar daga ranar 2 ga watan Afrilu zuwa jiya Litinin 25 ga wata ne sojojin Nijer da na Burkina Faso suka yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan da aka kiyasta cewa sun haura 100 yayin da wasu 40 da ake zargi da hada kai da ‘yan bindiga su ka shiga hannu.
Askarawan kasashen 2 sun yi nasarar ragargaza kayaki da dama da suka hada da bindigogi da motoci da sinadaran hada bom na gargajiya, lamarin da ya sa babban kwamandan rundunar mayakan Nijer, Janar Salifou Modi da takwaransa na Burkina Faso suka yi tattaki zuwa sansanin sojan hadin gwiwar da aka kafa a garin Dori domin jinjina wa baradensu, saboda gamsuwa da wannan jan aiki, koda yake soja 2 sun rasu wasu 2 sun jikkata.
Masu fashin baki irin su Moustapha Abdoulaye masani a sha'anin tsaro sun yaba da wannan galaba da sojojin suka samu?
Dimbin sojan kasa ne kowacce daga cikin kasashen 2 ta girke domin wannan aiki da ya gudana da gudunmowar sojan saman da suka rika yi wa sansanonin ‘yan bindiga luguden wuta, a cewar wannan Sanarwa, wace ta kara da cewa an kama galan galan na man fetur, da motoci, da makamai da dama. Shugaban kungiyar farar hula ta CADDED Son Allah Dambaji, na mai nuna farin cikin samun wannan nasara.
Wannan aikin kakkaba ya bada damar bude wa jama’a hanyoyin kai da kawo a tsakanin garuruwan yankin da abin ya faru ta bangaren Nijer da Burkina Faso, lamarin da ya saka walwala a zukatan al’umomin da abin ya shafa. Moustapha Abdoulaye na cewa wannan wata hujja ce da ke nuna mahimmancin samun hadin kai a tsakanin fararen hula da jami’an tsaro a yanayin da ake ciki a yau.
Yankin da Burkina Faso ke makwaftaka da Nijer, wani wuri ne da aka bayyana a matsayin mafi hadari da tashin hankali, sanadiyar yawaitar aika aikar ‘yan bindiga, inda ake bi gari gari a na karkashe mutane ana kuma datse hanyoyin zirga zirga don far wa matafiya, dalilin kenan da hukumomin tsaron kasashen 2 suka hada gwiwa don tsara wannan aiki da ya bada damar ragargaza sansanonin ‘yan bindiga da bayanai ke nunin sun ketaro ne daga arewacin Mali a wani lokacin da Faransa ta fara kwashe tarkacenta daga kasar, sakamakon rashin gamsuwa da hadin gwiwar da gwamnatin Mali ta yi da kamfanin sojan hayar Russia, wato Wagner.
Saurari cikakken rahoton Suleiman Barma: