Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Yi Ikrarin Rage Hare-haren 'Yan bindiga a Arewa Maso Yammaci


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa an rage samun hare-hare da masu satar shanu a yawancin yankin arewa maso gabashin kasar.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta mai dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar, John Enenche, ta bayyana cewa dakarun shirin "Hadarin Daji" ne ke da alhakin wannan nasarar.

Sanarwar ta nuna yadda aka samu raguwar ayyukan 'yan bindiga a jihohin Katsina, Kebbi, Zamfara da Sokoto a cikin wata daya.

"A hankali abubuwa sun fara komawa dai-dai a wadannan wuraren, manoma sun fara koma gonakkinsu yayin da sauran abubuwa suma suke kokarin komawa kamar da," a cewar sanarwar.

Dama dai rikicin 'yan bindiga a wadannan wuraren ya tilasta wa mutane da dama barin muhallansu da kuma gonakinsu.

Sanarwar ta alakanta wannan nasarar da yadda dakarun tsaron da aka jibge a yankin suke yaki da 'yan ta'addan ba kakkautawa.

Jihohin Zamfara da Sokoto da kuma Katsina sun kasance wuraren da ake yawan satar mutane domin neman kudin fansa a cikin kwanakin nan, lamarin da ke janyo zaman dar-dar a wadannan wuraren.

A baya, al'umomin yankin wadannan jihohi, sun yi ta korafin tabarbarewar sha'anin tsaro duk da cewa an jibge sojoji a yankunan, abin da har ya sa Majalisar Dattawa ta nemi manyan sojojin kasar su yi murabus.

Gabanin hakan ma, kamar yadda rahotanni suka nuna, shugaba Muhammadu Buhari ya sha kiran manyan jami'an tsaron kasar inda ya nuna musu fushinsa kan rashin tsaro da ya addabi arewa maso yammacin Najeriyar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG