Manjo Janar sojin Najeriya ne ya wakilci babban hasan sojan kasa na Nigeria Luet Gen Tukur Yusuf Buratai a kaddamar da wannan sabon shirin a garin Ngamdu dake da tazaran kilomita dari daga babban birnin Maiduguri .
Wakilin babban hasfan sojan Najeriyar ya bukaci jama’a su taimakawa sojoji a yaki da suke yi da ‘yan ta’adda da basu bayanai masu amfani ga aiki da suke yi kana ya yabawa shugabannin fararen hula a kan hadin kai da ake baiwa sojoji.
Kanal Sagir Musa darektan hulda da jama’a na rundunar sojan Najeriya, ya fadawa Muryar Amurka cewa a ranar 20 ga wannan Oktoba ne zasu fara wannan sabon shiri a kuma kammala shi ranar 31 ga watan Disamban wannan shekara.
Ya ce za a gudanar da shirin ne a ko ina a Najeriya domin rage barna ta yanar gizo. Ya kuma ce hukumar sojin Najeriya sashen kula da harkokin yanar gizo ta himmantu wurin dakile zuba labaran karya a yanar gizo da kuma wawashe dukiyar kasa ta wannan hanya.
Ya ce a karkashin wannan shirin sojin Najeriya zata bibiyi ‘yan ta’adda dake barin yankunan da suka boyewa suna shiga wasu wurare a cikin kasar domin gano su kuma aka kama su.
Wannan sabon shirin ma’aikatar sojan Najeriya na dakile miyagun ayyuka ta yanar gizo na zuwa ne yayin da ‘yan jihohin Borno da Yobe suke nuna damuwa a kan yanda ake rufe wasu manyan hanyoyin yankin lamarin dake haifar da tsadar abubuwan rayuwan yau da kullum.
Ga dai rahoton Haruna Dauda Biu daga Maiduguri:
Facebook Forum