A karkashin yarjejeniyar rundunar tsaron ta National Guard jihar Indiana ta amince domin baiwa sojojin kasar Nijar damar cin amfanin huldar dake tsakaninta da kasashe fiye da 70, wacce tun a shekarar 1993 ta bullo da wani shirin musamman, don kara karfafawa jami’an tsaron kasashen waje hazakar aiki.
Mataimakin shugaban rundunar Indiana National Guard, Janal Courtney P. Carr, yace wannan yajejeniyar dama ce gare mu baki ‘daya, mu karfafa dadaddiyar huldar dake tsakanin mu da wasu kasashen duniya.
Hafsan hafsoshin Nijar Seyni Garba, ya bayyana cewa kulla wannan yajejeniya wani abu ne da yazo akan lokacin da ake matukar bukata, bisa la’akari da mawuyacin yanayin tsaron da sojojin Nijar ke aiki a cikin sa, sakamakon ayyukan ta’addancin da ya addabi kasashen yankin Sahel da sahara.
Hulda a fannin aikin soja tsakanin dakarun Nijar da kasar Amurka wani abu ne mai dadaddan tarihi, to amma tallafin da Amurka a wannan fanni ya ninka a ‘yan shekarun baya bayan nan, bayan da hukumomin Nijar suka bukaci gwamnatin Amurka kan wannan bukata a shekarar 2015, saboda yadda barazanar tsaro ke karuwa a baki ‘dayan kasashen dake da Nijar.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.