Mai magana da yawun rundunar Kanar Sani Kukasheka Usman, ya ce a yanzu sojoji sun san dukkannin mabuyu da kuma sansanonin 'yan Boko Haram.
Gargadin na soji na zuwa ne a yayin da wasu tagwayen hare-hare su ka hallaka mutane akalla 9, tare da raunata wasu kuma 29, a arewacin Kamaru, harin da jami'an tsaron wurin ke dangantawa da kungiyar Boko Haram.
Kanar Usman ya ce mayakan sa kan sun shiga kunar bakin wake ne a matsayin hana ci gaba da yin tasiri, duk kuwa da cewa sojojin Najeriya sun yi matukar nakasa karfinsu.
"Kamar yadda ku ka sani, akwai wa'adin nan na Shugaban kasa cewa mu tabbata mun murkushe 'yan ta'addan Boko Haram kafin karshen watan Disamban 2015.
Saboda haka, mun yi ta aiki tukuru, kuma sannu a hankali, sun fara cim masu.” In ji Kukasheka.
Ya kuma kara da cewa, “Yanzu ya zama wajibi mu ankarar da al'umma , da ma 'yan ta'addan Boko Haram din cewa lokaci ya fa yi, da ya kamata su kwance damara; su kuma mika wuya kafin a karshe mu yi masu kaca-kaca."