Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Sakkwato Ta Nemi Hadin Kan Al'umma Wajen Hana ‘Yan Bindiga Abinci


Ahmad Aliyu
Ahmad Aliyu

Yayin da rundunar sojin Najeriya ke ci gaba da fatattakar 'yan bindiga dake addabar jama'a a yankin Arewa maso Yamma karkashin shirin Fansa Yamma, alamu na nuna ana samun galaba a kan 'yan bindigan

Ko a jiya Laraba jami'an tsaron al'umma da gwamnatin Sakkwato sun ce sun kama wasu mutane 13 da ake tuhumar masu sayo wa 'yan bindiga abinci da sauran kayan bukatun su.

Rundunar sojin Najeriya kwanakin nan ta yi ta fitar da bayanai masu nuna yadda ta ke ci gaba da kara kaimi wajen kai farmaki ga 'yan bindiga da ke addabar yankin arewa maso yamma kuma tana samun galaba, ta hanyar tarwatsa maboyar su, har ta ce ta hallaka wasu daga cikin kwamandojin hatsabibin dan ta'adda Bello Turji, da wasu 'yan ta'adda da dama.

Hakan ya sa 'yan bindigan suka tarwatse su ka watsu wurare daban-daban, suna neman mafaka domin su tsira da rayukan u, kuma hakan ne ya sa gwamnatin Sakkwato ta ankarar da jama'a musamman wadanda ke zaune a gabashin jihar wadanda su ne mafi kusa da inda barayin ke gudun ceton rai, da cewa su yi taka-tsan-tsan.

Yayin da ake sanya idon, sai aka samu nasarar damke wasu mutane kimanin goma sha uku da suka zo sayawa 'yan bindigar abinci.

Mai baiwa gwamnan Sakkwato shawara kan lamarin tsaro Kanal Abdul Usman mai ritaya yace jami'an tsaron al'umma da gwamnatin ta kafa ne suka kama mutanen bayan wasu bayanan sirri da aka samu.

Hakama an samu nasarar kubutar da wasu mutane da aka yi garkuwa da su a yankin Sabon Birni, baya ga wasu fiye da saba'in da aka ceto tsakanin watan Disamban bara da farkon wannan shekara.

Mazauna yankunan na gabashin Sakkwato inda matsalar rashin tsaro ta yi kaka gida yanzu suna cikin fara'a ganin yadda mahukunta suka yunkura da gaske domin samo mafita ga matsalar ta 'yan bindiga.

Da yake rundunar sojin Najeriya tace ko bayan kisan 'yan bindigar da ta yi akwai su da ta jikkata, a hare-haren da ta ke kaiwa, abin da masana tsaro ke ganin dole ne su bazu wasu wurare don neman agajin magani da abinci.

Akan haka ne gwamnatin Sakkwato ke neman hadin kan al'ummar gabashin yankin na Sakkwato.

Matsalar rashin tsaro dai ta jima tana ci wa jama'a musamman a arewacin Najeriya tuwo a kwarya, ta salwantar da rayukka da dukiyoyin jama'a da dama, ta tayar da garuruwa masu yawa, abinda kowa ke fatar ganin an magance.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammadu Nasir:

Gwamnatin Jihar Sakkwato Ta Nemi Hadin Kan Al'umma Wajen Hana ‘Yan Bindiga Abinci.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG