Wani sabon bincike ya gano cewa magungunan tarin fuka ko TB sun fi kashe kwayoyin cutar a berayen da ake gwaje-gwaje da su idan aka hada musu da sinadarin Vitamin C fiye da wadanda ba a hada musu da sinadarin ba.
Masana sun ce idan har hakan ya tabbata a jikin bil adam, to za a samu saukin jinyar cutar mai kisa da a kan kwashe watanni ana shan magani. Bugu da kari, amfani da sinadarin Vitamin C zai taimaka wajen shawo kan barazanar bijirewa magani da tarin fuka ke yi.
Tarin fuka yana kan gaba a cututtuka masu haddasa yawan mace-mace a duniya. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, a shekarar da ta gabata kimanin mutane miliyan 1.7 suka rasa rayukansu sakamakon cutar. Sama da mutane dubu 600 ne cikin sabbin mutane miliyan 10 da suka kamu da cutar ke da nau’in cutar da ta bijirewa magani.
Magungunan matakin farko da ake amfani da su, suna far wa kwayoyin cutar yayin da suke ninkawa a jikin mutum, amma kadan daga cikinsu suna rayuwa idan suka labe. Wadannan ne suke bullowa daga baya idan mutum ya daina shan magani inda suke zama nau’in cutar da ba ta jin magani.
A yanzu tsarin shan maganin tarin fuka yana daukan watanni 6 domin tabbatar da an kashe kwayoyin cutar kaf. Amma mutane basu son ci gaba da shan maganin cutar har na tsawon wa’adin da aka diba.
Facebook Forum