A Najeriya, Ministan watsa labarai na Najeriya Alhaji Lai Muhammed ya ce da shi da takwarorin aikinsa 43 sun sadaukar da kashi 50 cikin dari na albashinsu na watan Maris domin taimaka wa gwamnatin tarayya wajen yaki da cutar Coronavirus.
A sanarwar da Lai ya fitar, ya ce tuni har ministocin sun nada wani kwamiti a karkashin jagorancin karamar ministar sufuri Gbemisola Saraki wacce za ta gudanar da yadda za a hada kan gudunmawar.
Wannan matakin dai bai yi wa wata gamayyar kungiyoyin Arewa Maso Gabas dadi ba.
Lamarin da ya janyo ta kira taron manema labarai cikin gaggawa, inda ta bayyana takaicinta kamar yadda Alhaji Abdulrahman Buba Kwacham, wanda shi ne ya jagoranci gamayyar kungiyoyin, ya bayyana wa Muryar Amurka.
Kwacham ya ce wannan abin bakin ciki ne kuma abin takaici, domin shekara 11 kenan ana ta'addanci da kashe dubban mutane a shiyyar Arewa Maso Gabas da jihohin Zamfara, da Kaduna da Niger, amma babu Minista ko daya wanda ya yi irin wannan yunkuri da hada kudade masu yawa kamar yanzu.
Kwacham ya ce "dama su ne suke da ciwon, su ne masu tafiye tafiye a jiragen sama, kuma su ne suka kawo cutar, saboda haka suna tsoron kar ta kawar da su da iyalansu duka, shi ya sa suka bullo da wanan matakin."
To sai dai daya daga cikin jigajigan Jam'iyyar APC, kanar Garus Gololo mai murabus, ya ce wannan batu da kungiyoyin suka koka a kai gaskiya ne, "ya kamata gwamnoni da ministocin su bi abinda Gwamnan Jihar Legas ya yi wajen tanadar wa al'ummarsa abinci kafin ya kafa dokar hana fita, domin wani sai ya fita yake samo na abinci", a cewarsa.
A bangare guda kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa manyan 'yan Najeriya da suka tashi tsaye wajen yaki da annobar Coronavirus wacce aka fi sani da COVID-19.
Saurari wannan rahoton a sauti.
Facebook Forum