Shugabannin kasashen Larabawa sun hallara a garin Dhahran na Saudiyya domin halartar taron kolin kasashen Larabawa na 29, a yayinda ake ta maganganu dangane da mummunan halin da kasashe da suke yankin suke ciki. Shugabannin sun maida hankali kan rikici da kasashen da suke yankin suke yi da Iran,yaki da ake yi a Yemel,mummunar yakin basasar da ake yi a Syria, da kuma amincewar da Amurka ta yi cewa birnin kudus ne helkwatar kasar Isra'ila.
Kamar yadda wakilin Muryar Amurka Edward Yeranian ya aiko mana da rahoto daga birnin Alkhaira;
Sarki Abdullah na Jordan ya bada takaitaccen bayani kan muhimman batutuwa da kasashen Larabawa suke fuskanta,kamin daga bisani ya mika shugabancin taron ga Sarki Salman na Saudiyya, wanda shi ne mai masaukin baki na taron na kungiyar karo na 29.
Sarki Salman ya maida hankali kan batun birnin Qudus, wanda shine jigo a ajendar taron, da kuma kastalandan da yace kasar Iran tana yi cikin harkokin kasashen Larabawa.
Shugaban kungiyar hada kan kasashen Larabawa Ahmed Aboul Gheit ya soki shawarar shugaban Amurka Donald Trump na amincewa da birnin Qudus ya zama helkwatar kasar Isra'ila, ha kazalika ya koka da mummunan yanayin da kasar Syria take ciki.
Facebook Forum