Shugabannin al'ummar yankin na Gashaka sun zargi gwamnatin Taraba da yin watsi da wadanda suka rasa muhallansu sanadiyar rikicin kabilancin da ya barke makon jiya.
A taron manema labarai da hadakar kungiyar cigaban al'ummar Dolo suka kira a Jalingo fadar gwamnatin jihar shugabannin sun bukaci gwamnatin jihar ta kai masu dokin gaggawa ganin irin halin tagayyara da al'ummarsu ke ciki a yanzu.
Rabaran Joseph Nagombe Titus shugaban kungiyar ya bayyana halin da suke ciki a yanzu ya lissafa wuraren da mutanensu suka fake domin neman mafaka. Mutanensu sun gudu daga kauyuka hamsin da bakwai domin tserewa da rayukansu. Mutanen sun kai dubu goma .
Yace suna da kauyuka dari da goma sha shida. Wasu sun gudu zuwa wuraren da suke da 'yanuwa. Akwai kuma wadanda suke kan tsaunuka daga su sai bante.
Wannan matsalar ta samo asali ne sanadiyar rikicin Fulani makiyaya da al'ummar Dolo manoma.
Gwamnatin jihar ta musanta zargin cewa tana nuna bangaranci. Hadimin gwamnan ta fuskar labarai Sylvanus Giwa yace babu shakka an yi barna amma idan Allah ya yadda hakan ba zai kara faruwa ba. Yace ran gwamnan ya baci sosai. Hadiminn ya musanta batun goyon bayan wani bangare.
Ga karin bayani.