Dan majalisar wakilai Onarebu Garba Garba Cede ya kira 'yan jihar cewa dole ne su yiwa kansu karatun ta nastu idan har suna son jihar ta samu cigaba.
Yace idan ba zaman lafiya ko gona mutum ba zai iya zuwa ba. Ba za'a iya zuwa a yi sana'a ba. Harkokin sufuri zasu tsaya cik saboda babu zaman lafiya. Zaman lafiya nada mahimmanci ga rayuwar al'umma. Saboda haka yace dole ne ana bukatar wanzuwar zaman lafiya a jihar.
Shi ma Onarebul Umar Yusuf wanda yake wakiltar mazabar Gashaka a majalisar dokokin jihar yace hankula sun kwanta a yankin kuma alamura sun fara komawa kamar da biyo bayan rikicin da ya faru tsakanin Fulani da al'ummar Doro. Ya kira gwamnati ta tabbatar an samu dorewar zaman lafiya a yankinsu domin mutane su koma su cigaba da ayyukansu kamar noma.
A kananan hukumomi karama Lamido da Lau da suka yi fama da tashe-tashen hankula Onarebul Tanko da Giyel na cikin shugabannin al'ummomin yankin da suka rabtaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da suka yi a tsakaninsu. Sun ce wurkunawa da shomawa basu taba yaki da juna ba a tarihin yankin. Ko yanzu ma babu dalilin yin fada da junansu.Dole ne su zauna tare.
An kira al'ummomin Taraba gaba daya da su manta da abubuwan da suka faru can baya su dawo da dangantaka tsakaninsu kamar yadda suka gada daga iyaye da kakanni.
Ga karin bayani.
.