WASHINGTON, D.C —
Shugabannin Afrika baki daya ko kuma wakilansu na halartar wani kasaitaccen taro wanda ake nazari tare da yin bita a kan yaki da cututukan nan na kanjamau da tarin fuka da malariya watau zazzabin cizon sauro da manyan cututuka dake addabar kasashen Afrika. Kasashe 10 me suka yi jawabai masu karfin gaske a rana ta farko inda suka nuna muhimmancin hada kai da kuma gamsuwar da suka yi da kuma tabacin cewa, zasu tabbatar sun hada karfi da karfe domin a yaki wadannan cututukan daga cikin Afrika.
Kamar yadda shugabannin suka nuna ana sa ran lallai za a fito da cibiyoyi dabam dabam wadanda zasu yi nazari tare da binciko magungunan da Afrika da kanta zata kirkiro domin yaki da wadannan cututukan koma a aika da su kasashen keatare domin ciniki a kansu.
Daya daga cikin manyan jami'an da suka shirya wannan taron a shekara ta 2011, Professor Abdulsami Nasidi tace an sami ci gaba ya kuma bayyana muhimmancin taron na bana.