Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afghanistan Sun Cimma Matsaya Domin Kawar da Matsalolin Kasar


Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani da abokin hamayyarsa Abdalla Abdullah wanda suka raba iko tare bayan kiki-kakar siyasa a shekarar 2014
Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani da abokin hamayyarsa Abdalla Abdullah wanda suka raba iko tare bayan kiki-kakar siyasa a shekarar 2014

Jami’an kasar Afghanistan sunce shugabannin gwamnatin hadin kan kasa sun cimma matsaya cewa zasu hada hannu domin kawo karshen matsalolin tsaro da sauran wasu kalubale da suka addabi kasar da yaki ya daidaita.

Wannan dai yana zuwa ne kwana daya bayan da Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice, ta bayyana cewa yanayin siyasar kasar na iya rugujewa, musammam idan akayi la’akari da rashin jittuwar dake tsakanin shugaba Ashraf Ghani da Abdulah Abdallah wanda ke bukutar sulhu cikin gaggawa.

Kasar Amurka dai ce ta shiga tsakanin wannan kiki-kakan tsakanin Ghani da abokin hamayyarsa, domin ganin shugabannin biyu sun samar da gwamnatin hadin kan kasa a shekarar 2014.Wannan yarjejeniyar dai ta haifar da samar da ofishin babban jamii wanda ya raba iko da shugaban kasa.

Amma kuma daga bisani duka shugabannin biyu, Ghani da Abdallah suna sukan junansu da cewa kowanne ya kaucewa yarjejeniyar da aka kulla, kuma suna haka ne a bainar jama’a daidai lokacin da wa’adin gwamnatin na tsawon shekaru biyu ke kawo karshe cikin wannan watan.

Abdallah yace Ghani baya tuntubarsa akan wasu muhimmam batutuwan gwamnati musammam abinda ya shafi daukar aiki, haka kuma shugaban baya ko kokarin ganin an gyara dokokin zaben kasar domin gujewa abinda ya faru a zaben shekarar 2014.

Amma shugaba Ghani yayi fatali da wadannan zarge-zargen

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG