Yau shugabannin siyasa da na addini sunyi kira da a zauna laifya tareda yin addu’o’I na musamman a birnin na kano, bayan wani mummunar farmakin bama-bamai da yayi sanadiyyar mutane 170.
Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero tareda gwamnan jihar Alhaji Rabi’u kwankwaso sunyi addu’o’I a masallaci. Sai dai mun sami labarin cewa rabin masallacin babu mutane sabo da suna fargabar zuwa.
Kungiyar nan dake da’awar islama da aka fi sani da sunan Boko Haram, ta dauki alhakin kai harin na ranar jumma’a abinrin na kano, mai jama’a fiyeda milyan tara.
Jiya lahadi shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kai ziyara afadar sarkin Kano domin jajanta masa da al’umar jihar, ya kuma yi alawashin za a hukunta wadanda suka kai harin.
Shugaba Jonathan yana shan suka sabo da ya gaza shawo kan hare haren da mayakan sakai ke aunawa kan cibiyoyin gwamnati dan atsaro a fadin arewacin Najeriya.
Wani da yake ikirarin shine kakakin kungiyar ta Boko Haram yace harin da aka kai ramuwar gayyace sabo da kama ‘yan kungiyar a Kano.
Sojoji suna ci gaba da sintiri akan titunan birnin Kano a wunin litinin, suna baiwa mazauna birnin tabbacin zasu kare laifyarsu, duk da haka ana zaman dar dar sosai.