Zaman fargaba ta karu a yayinda aka dauki tsauraran matakan tsaro a Kano, birnin na biyu wajen girma a arewacin Nigeria, inda litinin din nan yan Sanda suka gano bama bamai guda goma da wasu nakiyoyin, a yayinda kuma yawan mutanen da suka mutu a sakamakon hare haren ranar juma'a suke ta karuwa.
Hukumomi sun baiyana cewa akalla mutane dari da tamanin da hudu aka kashe, yawancinsu farar hula a sakamakon tashin bama bamai da musayar harbe harben da aka dora laifinsu akan yan kungiyar Boko Haram.
Gwamnatin Amirka ta Obama tabi sahun sauran kasashen duniya, wajen yin Allah wadai da hare haren, wadanda galibi suka auna ofisoshin yan sanda da gine ginen gwamnati. Wata mai magana da yawur ma'aikatar harkokin wajen Amirka, Victoria Nuland tace Amirka ta damu ainun gameda wadannan hare haren. Tace Amirka zata tura masana dakile aiyukan ta'adanci zuwa Nigeria.
Litinin din nan ne kuma, shugabanin siyasa da addini suka taru domi yi adu'o'in samun zaman lafiya. To amma Masalacin da mai martaba sarkin Kano yake zuwa Sallah kusan fayau take, domin mutane suna jin tsoron fita.