Shugaban kasar Turkiyya Rajib Tayyib Erdogan, ya fara aiki tareda sabbin karin iko, a dai dai lokacind a kasar take komawa tsarin shugaban kasa mai cikakken iko.
"Nayi alkawarin karfafa hadin kai da dangantaka tsakanin mu," Erdogan, ya fadawa majalisar dokokin kasar jiya Litinin, bayan da yayi rantsuwar kama aiki na wani sabon wa'adi.Wakilai daga jam'iyyarsa ta AKP suna sowa, yayinda 'yan hamayya suna zaune shiru.
'Yan hamayya suna gargadin cewa Turkiyya tana fuskantar shugaba mai salon mulkin kama-karya, wadda jama'a suka zaba. Sai dai shugaba Erdogan ya dage cewa dumbin iko da ya samu a yanzu suna da muhimmanci domin tunkarar kalubale na rarrabuwar kawuna ta siyasa da kasar take fuskanta.
An kama daliban kasar 6 ranar Jumma'a, abikin saukar karatu saboda sun rike katon zane na ba'a ga shugaba Erdogan. Dukkan su suna fuskantar zargin zagin shugaban kasa. Wasu masu nazarin al'amuran yau da kullum suna jin shugaba Erdogan yana iya amfani da dumbin ikon da yake dashi ya magance matsalar rarrabuwar kawuna da kasar take fama dashi. Firai Ministan kasar mai barin gado Binali Yildrim ya nuna alamun cewa da shugaba Erdogan zai kawo karshen aiki da dokar ta baci.
Facebook Forum