Shugaban kasar Tanzania John Magufuli da ya yi fice wajen nuna shakku kan cutar COVID-19 a Afirka ya rasu.
Ya rasu yana mai shekara 61.
A ranar Laraba mataimakiyar shugaban kasa Samia Suluhu ta sanar da mutuwar shugaba Magufuli, wanda ta ce ya yi fama da cutar bugun zuciya.
Kamfanin dillancin labarai na AP ya ce a ranar Laraba mataimakiyar shugaban kasa Samia Suluhu ta sanar da mutuwar shugaba Magufuli, wanda ta ce ya yi fama da cutar bugun zuciya.
Karin bayani akan: Samia Suluhu Hassan, John Magufuli, da Tanzania.
Rabon da a ga Magufuli a baina jama’a, tun a watan Fabrairu kuma manyan jami’an gwamnatinsa sun musanta raderadin da ake yi cewa ba shi da lafiya, duk da cewa ana ta yadawa a kafafen sada zumunta cewa mai yiwuwa har ya fita a hayyacinsa sanadiyyar rashin lafiyar.
Marigayin na daya daga cikin fitattun mutane a nahiyar Afirka da ke nuna shakku kan cutar COVID-19.
A bara, ya fito ya bayyana cewa kasar ta Tanzania ta kawar da cutar baki daya bayan kwana uku da aka kwashe ana addu’o’i a kasar.