Yayin da yake wani jawabi a taron samar da tsaro yankin a Tajikistan, Putin ya ce shugaba Assad a shirye ya ke ya yi aiki da ‘yan adawa, kan yadda za a shawo kan matsalar rikicin siyasar kasar, ammam dole ne ya fara da kawar da barazanar ‘yan tadda.
Shugaba Assad dai ya jima yana amfani da Kalmar “’yan tadda” akan ‘yan tawayen kasarsa dake adawa da mulkinsa, baya ga kungiyar ISIS da ta mamaye wasu yankunan kasar da dama.
Putin har ila yau ya yi watsi da kalaman da wasu ke yi na cewa shigar Rasha cikin rikicin Syrian ya kara haifar da kwararar ‘yan gudun hijra.
Ya kuma ce da-a-ce Rasha ba ta sa baki a rikicin ba, da yawan bakin hauren da ke zuwa nahiyar turai sun fi haka.
Waddanan kamalamai na Putin na zuwa ne, kwana guda bayan da Ma’aikatar tsaron Amurka ta tabbatar da cewa Rashan na kokarin gina sansanin soji a Syria.