Shugaban da ya sauka a filin jirgin sama dake garin Bauchi ya zarce zuwa Azare domin ganin irin barnar da gobara ta yiwa kasuwar garin.
Haka kuma shugaban ya ziyarci fadar sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleimanu Adamu inda ya mika gaisuwarsa.
Yace ya ga irin barnar da gobara ta yi a kasuwar Azare da fatan Alla zai maida masu abun da ya fi asarar da suka yi. Ya karfafa musu gwiwar yin addu’a saboda bala’in da ya faru ya fi karfin mutum
Shugaba Buhari ya yiwa wadanda abun ya shafa jaje da ta’aziya.
Shi ko gwamnan Bauchi Barrister Muhammad Abdullahi Abubakar ya bayyana ziyarar ta shugaban kasa a matsayin ta soyayya ce. Ya ce tun kafin shugaban ya kawo ziyarsa ya ce a mikawa mutanen jihar jajensa. Bayan haka shugaban ya aika da wata tawaga a karkashin jagorancin ministan ilimi da shugaban hukumar bada agajin gaggawa zuwa jihar.
Gobarar ta lakume akalla shaguna dari biyar musamman, shagunan sayar da kayayyakin abinci da tufafi. Yawancin ‘yan kasuwan a Kano suke karbo kaya kuma sai sun sayar su mayar da kudin.
A saurari rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani
Facebook Forum