Alhamis mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bude taron ministocin tsaron kasashen yankin Sahel a Abuja.
Mataimakin y ace tun bayan juyin-juya halin da aka yi a kasashen Larabawa da kuma rushewar gwamnatin Moammar Ghadafi a Libya aka shiga rudani.
Yace kasashe irin su Najeriya, Mali, Burkina Faso da Niger sune suka fara fuskantar matsalolin masu tsatsauran ra’ayi da ‘yan ta’adda, lamarin da ya zama babban barazanar tsaro ga yankin Sahel.
A nasa bangaren sakataren kasashen Sahel da Sahara Ambassador Ibrahim Sani Aban ya yi tsokaci kan matsalar ‘yan Boko Haram da yadda shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya jagoranci karya lagonsu a yankin tafkin Chadi.
Farfesa Osinbajo yace abu ne mai karfafa gwuiwa domin cimma gagarumar nasara wajen shawo kan ‘yan Boko Haram da kuma hobasan da rundunar yankin tafkin Chadi keyi. Kokarin sojojin ne ya dakile ayyukansu.
Jim kadan bayan bude taron ministan tsaron kasar Niger Mukhtari Kalla ya yi wa Sashen Hausa bayanin taron ya kunshi mutanen kasashen Sahel da Sahara kuma shin a bakwai da zasu yi. Sun kira taron ne domin su tattauna matsalolin ta’addanci da sauran ayyukan asha da ake aikatawa.
Kasashen 25 ne ke halartar taron, yayinda kasashen Rasha, Birtaniya, China, Saudiya,da kungiyar Tarayyar Afirka, AU da Majalisar Dinkin Duniya, MDD ke zaman ‘yan kallo.
A saurari rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani
Facebook Forum