A taron an amince cewa za'a hada gwiwa tsakanin duka jami'an tsaron Najeriya domin a tabbatar an yaki bazuwa ko shigowar annobar nan ta ebola wadda ta fara yin barna a kasashen yammacin Afirka dake makwaftaka da kasar.
Tun farko shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan yayi ganawar domin a tattauna tsakanin duk jami'an tsaron kasar domin su tsara su kuma amince da matakai na bai daya da hukumomin zasu yi anfani dasu domin a tabbatar an fuskanci wannan sabuwar kalubale akan lokaci ba tare da bazuwar annobar a kasar ba.
Shugaban hukumar kwastan ta Najeriya Abdullahi Dikko Inde ya bayyana wa manema labaru a Abuja cewa tabbas an yi ganawar da shugaban kasa inda shi kansa yake bada shawarar cewa wajibi ne a yanzu kowane jami'in tsaro ya ja da baya ya bar jami'an kiwon lafiya su fara mu'amala da duk wadanda suka shigo kasar. Bayansu sai sauran jami'an tsaro su yi nasu aikin da doka ta tsara masu. Idan jami'an kiwon lafiya sun samu wanda basu yadda ya shigo ba sai a hadashi da likitoci.
Taron farko da aka yi da shugaban kasa ya fitar da kudi masu yawa domin ma'aikatar kiwon lafiya ta sawo naurori da duk kayan aikin da take bukata da ma abun da zai kare su masu aikin kiwon lafiyan. Cutar idan bata yi tsanani ba ana iya warkar da ita.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.