Da misalin karfe goma sha daya agogon Najeriya ne shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya sauka Yaunde babban birnin kasar Kamaru.
Shugaban kasar Paul Biya shi ne ya karbeshi a filin jirgin sama dake birnin.Daga filin ne suka je masauki a Otel Hilton dake birnin. Daga otel din sun tafi inda shugabannin biyu suka tattauna a asirce.
Shugaban Najeriya zai gana da 'yan Najeriya mazauna kasar ta Kamaru a ofishin jakadancin Najeriya dake Yaunde. 'Yan Najeriya daga wasu garuruwan kamar Duala da dai sauransu zasu halarci taron ganawa da Shugaba Buhari.
Maganar tsaro ce take kan gaba a tattaunawarsu. Bayan maganar tsaro sai ta kasuwanci saboda akwai 'yan Najeriya sama da miliyan hudu dake zaune a kasar yawancinsu kuma 'yan kasuwa ne.
Ana shirin gina hanyoyi da zasu je Enugu da Abakaliki a kudancin Najeriya. Ta arewa kuma akwai wata hanya da zata shiga jihar Adamawan Najeriya. Zasu tattauna akan wadannan saboda bunkasa kasuwanci tsakanini kasashen biyu.
Batun yankin Bakasi ya kawo matsala tsakanin kasashen amma sun shawota. Kafin yaduwar kungiyar Boko Haram kasar Kamaru sojoji kadan gareta amma yanzu ta kara daukan wasu. Kasar ta kafa makarantar koyas da aikin soja kuma tana daukan matasa.
Ga karin bayani.