WASHINGTON, DC —
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon na ci gaba da rangadi a kasashe biyar na Afrika da Sahara. Shugaban na Majalisar Dinkin Duniya zai isa kasar jamahuriyar Nijer ranar laraba tare da tawagar shi wadda ta kunshi shugaban Bankin Duniya, da shugabar kungiyar kasashen Afirka, da shugaban bankin raya kasashen Afrika da kwamishinan harakokin bunkasa kasa na Tarayyar Turai. Su na rangadin ne a kasashen biyar da zummar girka wani tsarin samar da ci gaba mai dorewa da kuma rage radadin talauci a kasashen masu fama da rigingimu da tashe-tashen hankula, baicin haka kuma kasashen biyar na fuskantar matsalolin safarar makamai, da na bil Adama da kuma masifar ta’addanci. Kasashen biyar su ne Mali da jamahuriyar Nijer da Chadi da Burkina Faso da kuma Mauritania. Wakilin Sashen Hausa a Niamey babban birnin kasar jamahuriyar Nijer, Abdoulaye Mamane Amadou ya aiko da rahoto:
Larabar nan tawagar shugaban na Majalisar Dinkin Duniya za ta isa kasar Nijer bayan ta je Mali