WASHINGTON, DC —
Jam'iyar ARD Adalci-Mutunci mai akidar gina kasar jamahuriyar Nijer, wadda kuma ba ta goyon bayan kowane bangare a kasar ta yi babban taron na musamman a birnin Konni inda ta zabi sabbin shugabannin kuma ta tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban kasar jamahuriyar Nijer. Halima Djimrao ta tattauna da Abba Moussa Abdoulaye wanda aka fi sani da sunan Magaji, jigo kuma mai fada a ji a jam'iyar ta ARD Adalci-Mutunci. Magaji ya fara da kara jaddada abubuwan da suka tattauna a kai a lokacin babban taron da suka yi kwana biyu su na yi a birnin Konni, jahar Tahoua.
Jam'iyar ARD Adalci-Mutunci ta kammala babban taron ta tare da zaben sabbin shugabanni da kuma yin kira ga magabatan kasar jamahuriyar Nijer
Labarai masu alaka
Nuwamba 09, 2024